A yau Talata ne 14/02/2023 ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar China , ya kira wani taro, inda ya yi bayani kan yadda za a kara farfado da ayyukan gona a dukkanin kauyukan kasar.
Yayin taron, yayi bayyana cewa, an gudanar da ayyuka masu nasaba da aikin gona, da raya kauyuka, da manoma yadda ya kamata a kasar a shekarar da ta gabata, inda yace lamarin ya taimaka sosai wajen kawo ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al’umma a kasar.
A cewar rahoton Adadin hatsin da aka samu a kasar China bara, ya kai kilo biliyan 686.5, a bana kuma adadin ya karu da kilo biliyan 3.7, kuma ya kai matsayin koli a tarihi.
Kaza lika yace zasu ci gaba da tabbatar da sakamakon da aka samu wajen yaki da talauci, yayin da kudin shigar manoman kasar zai riga karuwa sannu a hankali, inda matsakaicin kudin shigar ko wanen manomi a duk shekara, zai kai sama da kudin yuan dubu 20, adadin da ya karu da kaso 4.2 idan aka kwatanta da na shekarar 2021.
Bugu da kari, an kara fardado da kauyuka a sassan kasar lami lafiya, tare kuma da ciyar da sana’o’in kauyukan gaba yadda ya kamata.