A yau ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi bayani game da nasarorin da Sin ta samu, wajen gudanar da ayyukan taimakawa kasashen waje a fannin ba da jinya, inda ya ce taimakawa kasashen waje a fannin ba da jinya, muhimmin aiki ne a cikin ayyukan taimakawa kasashen waje.
Tun da Sin ta tura rukunin farko na aikin ba da jinya ga kasar Algeria a shekarar 1963, har zuwa yanzu, ta riga ta tura jimillar ma’aikatan jinya dubu 30 ga kasashe da yankuna 76 a duniya, wadanda suka ba da jinya ga mutane marasa lafiya miliyan 290.
A kwanakin baya, babban sakataren JKS Xi Jinping, ya amsa wasikar da membobin rukunin aikin ba da jinya na Sin dake aiki a kasar Afirka ta Tsakiya suka rubuta masa, inda ya gaishe da daukacin membobin rukunonin aikin ba da jinya na kasar Sin dake kasashen waje. Ya kuma ce shekarar bana ita ce ta cika shekaru 60, tun bayan da Sin ta tura rukunin aikin ba da jinya na farko zuwa kasashen waje.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, a fannin kiwon lafiya, ciki har da aikin taimakawa kasashen waje a fannin ba da jinya, don gina gadar kiwon lafiya a tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a kara samar da gudummawar tabbatar da kiwon lafiyar jama’ar dukkanin duniya, da kuma sa kaimi ga raya tsarin kiwon lafiyar bil Adam baki daya.