Babban limamin cocin Deeper Christian Life Ministry, Fasto William Kumuyi, ya bayyana cewa Allah bai yi masa wahayi game da wanda zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba ba.
Kumuyi ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, jihar Neja yayin wani taro da ya gudana a ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba.
Jaridar legit hausa ta ruwaito cewa Faston ya yi alkawarin bayyanawa duniya da zaran Allah ya sanar da shi wanene shugaban kasar Najeriya na gaba, jaridar.
Kumaye yace “Ba zan gaya maku karya ba. Allah bai nuna mun komai ba. Bai ga dacewar fada mani ba. Baya so ya sanar da kowa, komai. Wanene ni da zan ce ma Allah, me yasa baka fada mani shugaban kasa nag aba ba? Idan ya sanar da ni, zan fito na fada maku.”
Ya kuma yi kira ga matasan da suka kai shekarun zabe da su fito a ranar zabe sannan su zabi yan takarar da suke muradi wadanda suke ganin za su kai Najeriya matakin da take fatan kaiwa,