Manchester City ta tsawaita kwantiragin Foden, Rangers za ta cefanar da Kamara.

Daga Walif Hari

Manchester City ta cimma matsaya a kan sabon kwantiragin dan wasan tsakiyar Ingila Phil Foden, inda an yi amanar cewa wa’adin kwantiragin ya kai shekara 6 kuma za a a rika biyansa fam dubu 250 a kowane mako . (Football Insider)

Dan wasan Belguim Romelu Lukaku ba shi da aniyar komawa Chelsea idan wa’adin da aka ba da shi aro ga Inter Milan ya zo karshe wadda ake sa ran za ta sabunta kwantiragin dan wasan mai shekara 29. (La Gazzetta dello Sport, via Football Italia)

Dan wasan baya na Liverpool Vigil Van Dijk mai shekara 31 ya yi amannar cewa dan wasan baya na kasar Holland Jurien Timber wanda aka alakanta shi da komawa Manchester United a bazara ya samu kwarewa sosai fiye da lokacin da ya ke shekara 21. (Manchester Evening News)

Dan wasan bayan Argentina Lisandro Martinez mai shekara 24 ya ce bai kula da sukar da ake masa ba a farkon kakar wasa ta bana bayan komawarsa Manchester United daga Ajax a bazara .

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments