Nigerian Air Limited ya fara daukar maaikata

Daga Sadiq Lamin Has n

Kamfanin sufurin Jiragen Sama na Najeriya mai suna Nigeria Air Limited, ya fara ɗaukar matuƙa da sauran ma’aikatan jiragen, saboda fara zirga-zirga nan bada jimawa ba bayan an ƙaddamar da shi a kwanaki masu zuwa.

Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ce ta fitar da wannan sanarwar a shafin ta na Tiwita a ranar Juma’a.

“A yanzu Najeriya ta fara aikin fara horas da matuƙa jiragen sama da sauran ma’aikatan jirgin.

Ana neman irin waɗanda su ka ƙware a tuƙin jirgin sama da kwarewa a wasu ayyukan jirgin.

Waɗanda ake neman sun haɗa da ƙwararru a matakin B737 Kyaftin; Ƙwararru a matakin B737 Kyaftin na Matakin Farko da kuma Manyan Matuƙa Jirgi da Injiniyoyi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Muƙaman dai a Birnin tarayya Abuja ake buƙatar su da kuma jihar Legas. Kuma akwai albashi mai tsoka.

Sanarwar ta ce idan aka shiga manhajar www nigeriaair.world nan gaba kaɗan, za a ga wurin da za a shiga a cika fam.

Wanda duk ke ganin ya cancanci wannan aiki, sai ya aiko da takardun bayanan sa a recruitment@nigeriaair.world.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a bi sunayen waɗanda ke neman aikin a tsanake domin a tantance waɗanda za a ɗauka bisa cancanta. Za a kira waɗanda aka ɗauka domin a yi masu intabiyu ido-da-ido.

Sannan kuma waɗanda ba a ɗauka ba, za su ji shiru, ba za a koma ta kan su ba.

A ranar 18 Ga Yuli, 2018 aka ƙaddamar Nigeria Air a wani filin jirgin sama na Famborough da ke Ingila.

Sai dai an jingine batun bayan da aka riƙa sukar shirin cewa ba shi da wani muhimmanci, kuma ba mai ɗorewa ba ne.

A wancan lokacin dai an ce za a kashe dala miliyan 8.8 wajen fara ƙaddamarwar. Idan za’a fara shirin kuma zai ci dala miliyan 300.

Cin hanci da rashawa ne ya kashe Kamfanin Nigeria Airways shekaru masu yawa da su ka gabata.

Wannan sabon kamfanin sufurin jiragen sama dai mallakar Najeriya ne da Ethiopian Airlines, wanda kamfanin na Ethiopia ke da kashi 49 bisa 100 na jarin sa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments