Gamayyar kungiyar matasan PDP ta Arewacin kasar nan sun gudanar da zanga zanga a kofar shiga garin Katsina a ranar Lahadi, suna masu neman Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya sauka.
Fusatattun matasan, wadanda ke dauke da kwaleyen rubutu iri-iri, sun ce lallai sai an cire Ayu daga kujerar mulki kafin zaben 2023.
Sun dauki kwalaye kamar su: ‘Dole Ayu yayi murabus’, ‘PDP ba kamfanin mai zaman kansa bane’, Ka cika alkawarinka’, ‘matasan Arewa: mu masu son gaskiya da adalci ne.
Shugaban gamayyar kungiyar, Shehu Isa Dan’Inna, yayi jawabi ga manema labarai a yayin zanga zangar ya ce dole shugaban jam’iyyar ta PDP na kasa yayi murabus sannan ya daina daukar kansa a matsayin Shugaban jam’iyyar don dakile rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
Ya ce kamata yayi Ayu ya cika alkawarin da ya dauka na yin murabus da zarar an kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Jaridar Thisday ta ruwaito. Dan’Inna na cewa: “Muna kira ga shugaban jam’iyyar na kasa da ya cika alkawarinsa. Ayu ya bayyana cewa da zaran an kammala babban taron idan dan arewacin Najeriya ya zama mai rike da tutar PDP zai yi murabus.