Majalisar dokoki ba ta bin diddigin yadda ake aiwatar da kasafin kudi.

Daga Walid Hari.
Masana a Najeriya sun fara tsokaci kan gazawar majalisar dokokin kasar wajen bin diddigin yadda ake aiwatar da kasafin kudi a shekarun da suka gabata.
Dr Ibrahim Shehu, malami a sashen koyon aikin gwamnati na jam’iar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma mai bincike kan yadda ake aiwatar da kasafin kudin na Najeriya, ya ce sun samu bayanai a kan in da majalisar ta gaza, wato babban zauren majalisar ba ya zama yana duba irin korafe-korafen da ake na gazawa wajen aiwatar da kasafin kudin.
Dr Shehu ya ce kwata-kwata ba a yin abin da ya kamata a majalisar.
Ya kara da cewa” Da majalisar tana duba irin wadan nan rahotanni, to ko shakka ba bu da shugabanni hukumomi da ma’aikatun gwamnati za su shiga taitayinsu.
A makon da ya gabata ne dai shugaban Najeriya ya gabatar wa zauren majalisar kasafin kudi, wanda ya kunshi kudi sama da naira tiriliyan ashirin, kuma shi ne kasafin kudi na karshe da shugaban zai gabatar kafin saukarsa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments