Kasuwar cinikayyar yan wasan kwallan kafa.

Daga Walid Hari.
Chelsea na neman sayen ɗan wasan tsakiyar Villarreal Yeremy Pino, 19, don maye gurbin ɗan wasan tsakiyar Ingila Mason Mount da ke shiga watannin ƙarshe na kwantiraginsa. Chelase kuma na neman Lorenzo Pollegrini, 27 ɗan wasan tsakiyar Roma. (Telegraph)
Arsenal ta nuna sha’awar sayen dan wasan gaban Bruges Feran Jutgla, 23. (Totofichajes)
Liverpool na iya duba yiwuwar sayen dan wasan gaban Belgium Jeremy Doku, 21 a Janairu, (Calciomercato – in Italian)
AC Milan na duba yiwuwar sayen dan wasan Chelsea Hakim Ziyech, 29 a watan Janairu. (Tuttomercatoweb – in Italian)
Inter Milan kuwa ta shirya son kwadaitar da ɗan wasan baya na Netherlands, Nathan Ake, 27 daga Manchester City. (Ekrem Konur on Twitter)

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments