Yadda aka sa wa yara 175 cutar HIV da gan-gan a kasar Birtaniya.

Daga Walid Hari.
Sama da kananan yara 150 masu fama da cutar borin jini ne aka saka wa cutar HIV a tsakanin shekarun 1980s, kamar yadda wani kundin Tattarai Bayanai na kasar ya fada.

Wasu daga cikin iyalan da lamarin ya shafa suna bayyana hujjoji ne a gaban kwamitin binciken lamarin, wanda ake gani a matsayin bala’in mafi muni a tarihin Hukumar Lafiyar ta Kasar.

A tunanin Linda,wadda mahaifiyace ga wani yaro za a mata batun mayar da danta zuwa babban asibitin Sarauniya Elizabeth ne da ke cikin birni.

A tsakanin 1970 zuwa 1991, mutum 1,250 masu fama da matsalolin jini sun kamu da cutar HIV bayan sun yi amfani da maganin Factor VIII, wanda sabon magani ne da ke sauya sinadarin da ke sa wa jini ya yi guda-guda a jikin dan Adam.

Haka kuma ana zargin dubbai sun kamu da cutar hepatitis C, wadda za ta iya shafar kodarsu da kuma kansa, ko dai ta hanyar amfani da maganin ko kuma wajen karin jini.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments