Gwamnatin Gambia ta kafa wani kwamitin hadin gwiwa mai kunshe da mambobi 11, domin bincike kan zargin yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a makon da ya gabata.
Kakakin gwamnatin kasar Ebrima Sankareh, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, masu binciken na da kwanaki 30, farawa daga jiyan, domin bincike da shirya rahotonsu, tare da gabatar da shi.
Kawo yanzu, kasar dake yammacin Afrika ta tsare sojoji 8 da farar hula guda, wadanda ake rike da su domin bincike