An shawarci shugabanni da yansiyasa a fadin kasar nan, da su rika tunawa da ‘ya’ya mata a kodayaushe domin irin gudunmawar da suke bayarwa a kodayaushe,musamman a lokutan zabe.
Shugaban harkokin mata ta kungiyar kasuwar singa kuma, yarsiyasa a jamiyyar APC hajiya Maryam Musa Gawuna ce,ta ba da wannan shawarar A zantawarta da Aksammedia  dangane da yadda aka wofantar da mata a alamuran siyasa Wanda akasari mata ne suke jajircewa wajen ganin sun mallaki katin zabe tare da yin tsayin daka domin yin zabe a lokuta daban_daban.
Hajiya Maryam Musa Gawuna, tana yin kira ga shugabannin da suke jagorantar Alumma, da su rika tunawa da mata wajen ganin an dama da su a harkokin kasuwanci da shugabanci ta yadda za, a dama da su kamar sauran kasashen Duniya.
Shugabar matan tace, yanzu lokaci ya canza,haka kuma,ita kanta siyasar ta sauya kamata yayi a baiwa mata dama sakamakon gudunmawar da suke bayarwa a fannonin ci gaban dimokaradiyyar kasar nan, inda tace,mata suna da rawar takawa a duk lokacin da aka basu dama domin nuns tasu basirar.
Haka zalika,Maryam Gawuna, ta bukaci mata da sauran alummar da su zage damtse wajen mallakar katin zabe,kasacewar da shine za su samu damar sauya Shugabannin da suke da bukatar su shugabancesu da yakinin za su kawo sauyi da ci gaba maidorewa a fadin kasar nan.
/Cov/Ibrahim Sani gama/