Wata jami’a dake kasar Amuruka Mai suna Crown University International ta karrama Falakin Shinkafi Amb. Yunusa Yusuf Hamza da lambar karrama Mafi girma ta Dakta.
Sanarwar karramawar na dauke ne cikin wata wasika mai kwanan watan 07 ga watan Yunin shekara ta 2023, Mai kuma dauke da sa hannun Magatakardar jami’ar Farfesa Sir Abhiram kukshicshka.
A cikin wasikar an bayyana cewa dukkanin Masu ruwa da tsaki a jami’ar sun amince da karramawar sakamakon an yi bisa chanchantar wanda aka karrama din wato Amb. Yunusa Yusuf Hamza, kuma lambar girmamawar ta sami amincewar duk wasu hukumomi Masu lura da irin wannan lambar yabo na kasar Amuruka.
jami’ar ta Crown University International wadda ke da reshe a nan Nigeria, tace ta karrama Falakin Shinkafi ne sakamakon wasu abubuwa da takai la’akari da shi wadanda suka hadar da taimakawa Masu Karamin karfi don ganin sun sami nagartacce Ilimi domin cigaban al’umma.
A lokuta daban-daban kungiyoyi da hukumomi a Kasar nan sun karrama Falakin Shinkafin sakamakon gudunmawar da yake bayarwa wajen ingata rayuwar mata, marayu da matasa musamman ta fuskar Ilimi da sana’o’in dogaro da kai.
Wannan karrama da Falakin Shinkafin ya samu ta nuna cewa daga yanzu za’a rika hada sunansa kamar haka Amb. (Dr) Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi.