Liverpool da Man U na zawarcin Bellingham, Ziyech na son barin Chelsea.
Daga Walid Y Hari.
Liverpool ce kan gaba a rige-rigen da take yi da Manchester United wajen neman dan wasan Borussia Dortmund kuma dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19. (Telegraph)
A gefe guda kuma Liverpool na tunanin zawarcin dan wasan Wolves kuma dan wasan tsakiya na Portugal Matheus Nunes, mai shekara 24 domin maye gurbin Bellingham. (UOL, via Mirror)
Dan wasan gefe na Chelsea Hakim Ziyech, mai shekara 29 na son barin Stamford bridge a wannan bazarar yayin da tsohon kulob dinsa Ajax da AC Milan na son dan wasan kasar Morocco ya taka masu leda. ( Football London)
Chelsea ta nemi a cefanar mata da dan wasan gaban AC Milan da Portugal Rafael Leoa, mai shekara 23 a cikin kasuwar bazara a cewar daraktan kulob din Paolo Maldini. (FourFourTwo)
Za a ba kocin Man United Ten Hag fam miliyan 70 don kashewa a kasuwar musayar‘yan wasa ta Janairu kuma adadin zai iya fin haka idan dan wasan gaba Cristiano Ronaldo ya bar kulob din