Mataimakin Gwamnan Dr.Nasuru Yusuf Gawuna, ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da kungiyar A p c one family Wanda ya gudana a Gidan Gwamnatin Kano.
Daga Ibrahim Sani gama.
Yace,babu shakka wannan kungiya za ta samu duk kulawar da ta kamata kasancewar akwai jigajigan mutane dake cikin wannan kungiya,ta hada wakilai Daga kananan hukumomi 44 dake jihar Kano domin zuwa marawa tafiyar jamiyyar APC da Dantakarar Gwamnan Kano da mataimakinsa Murtala Sule Garo da sauran yantakarkaru na jamiyyar APC.
Ya yi fatan wannan kungiya za ta tsaya tsayin daka wajen Samar da hadin kan yanjamiyya da sauran alummar da suke wajen jamiyyar, domin shigo da su tafiyar Dr Nasuru Yusuf Gawuna, domin ganin ya zama Gwamnan Kano.
A jawabinsa tun da farko Shugaban kungiyar APC One family, kuma, mataimakawa Gwamnan Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje, da shawara tun daga tushe Alh. Yusuf Abdullahi Timfafi, ya ce makasudun kafa wannan kungiya shi ne domin ganin an tallafawa tafiyar Dr Nasuru Yusuf Gawuna ya zama Gwamnan Kano a 2023.
Ya yi kira ga yanjamiyyar APC da su zo domin hada kai wajen Samar da manufa kwaya daya da za ta taimakawa jamiyyar APC a kakar zabe mai zuwa.
Ya shawarci Dantakarar Gwamnan Kano Dr. Nasuru Yusuf Gawuna, da ya zauna da Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinan yada labarai domin kawo daidaito ga yansocial media domin kaucewa kazafi ko cin mutuncin wani danjamiyya.