El-Rufai ya kaddamar da mika takardun mallaka na shaguna ga ‘yan kasuwa
Daga Sunusi Shehu Bako.
Gwamna Nasuru El-Rufai na jihar Kaduna ya mika takardun mallaka na shaguna ga ‘yan kasuwar da suka mallaki shaguna.
karkashin tsarin shirin da gwamnatin sa ta fito da shi na mallalka wa asalin ‘yan kasuwa shagunan da suke kasuwanci.
yan kasuwa da dama a Kasuwar Sheikh Abubakar Gumi. Wanda a baya mafi yawan su haya suke a cikin shagunan da suke kasuwanci a wannan Karo sun rabauta da mallakar na kan su.
Kuma wannan shirin ya shafi ‘yan kasuwar Sheikh Abubakar Gumi da sauran sababbin kasuwannin da ake ginawa a fadin jihar.
Gwammantin Jihar Kaduna ta yi tsari ne na ‘mortgage’ wato na tallafi yadda bankuna suka biya wa ‘yan kasuwan kudaden shaguna domin su sami damar mallakar shagunan da suke ciki, su kuma ‘yan kasuwan su biya bankuna cikin shekara bakawai.