M Yadda tsadar rayuwa ta tilastawa likitocin Najeriya ficewa zuwa ƙasashen waje
Najeriya dai ta kasance ƙasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, sannan ta na shirin fara fitar da sabbin takardun kuɗi karon farko cikin sama da shekaru 20.
Matakin dai wani yunkuri ne na sake dawo da kwarin gwiwa a kan kuɗin naira, da ke fuskantar matsin lamba.
Yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 20, mutane na ta kokawa kan yanayin tsadar rayuwa.
Hakan kuma ya sanya kwararrun matasa da suka ƙware a bangarori da dama barin ƙasar a cikin shekarun nan.
“Ka yi tunanin zuwa sayar da kayayyaki wata rana, kwatsam sai ka samu komai ya ninka har sau uku, ya mutum zai yi? Kana da iyali a gida. Me za ka fasa saya?” Oroma Cookey ta faɗa min a tattaunawa ta intanet da muka yi.
Mai zanen kayan kwalliyar ta bar babban birnin Najeriya, Legas, tare da iyalanta shekara guda da ta wuce zuwa babban birnin Birtaniya, Landan.
Mijinta wanda kuma ya kasance abokin kasuwancinta mai suna Osione, wanda mai zane ne, an ba shi bizar kwararre ta duniya, wanda ke bai wa shugabanni a fannin ilimi, fasaha da al’adu, da fasahar dijital yin aiki a Birtaniya.
Ta ce akwai wahala matuka wajen samar wa iyalanta rayuwa mai inganci a Legas.
“Kuɗin mu na sayo mana ƙananan abubuwa, ba mu iya biyan kuɗaɗen mu, ba mu iya yin abubuwan da muka saba yi.”
Oroma ta yi karatun a bangaren shari’a a Jami’ar Northumbria ta kasar Birtaniya, sannanta koma Najeriya kusan shekaru 20 da suka gabata, inda take da zimmar son yin amfani da karatunta wajen ci gaban ƙasarta.
Oroma tare da Osione, sun kirkiro da This Is Us, wani samfurin salo da salon rayuwa mai ɗorewa wanda ke amfani da kayan gida da masu sana’a, wanda ya kunshi auduga da ake nomawa da kuma rini a arewacin Najeriya.
Da farko, matsalar tsadar rayuwa ba ta shafe su ba.
“Saboda muna da abin da muka dogara da shi a Najeriya, abubuwa ba su yi mana muni ba kamar sauran mutane,” in ji Oroma.
“Don haka lokacin da kowa ke ƙara farashinsa, mun tsallake karin saboda muna da ɗan abin dogaro