Alkaluman ma’aikatar cinikayyar kasar China sun nuna yadda adadin sayayyar amfanin gona ta yanar gizo ta karu da kaso 9.2 bisa dari a shekara guda, inda a bara darajar sayayyar ta kai kudin Sin yuan biliyan 531.38, wato kwatankwacin dalar Amurka biliyan 78.58.
Alkaluman sun nuna karuwar da fannin ya samu da sama da kaso 6.4 bisa dari, idan an kwatanta da na shekarar 2021.