Dangantakar Putin da Erdogan ta dogara ne akan amincewa da juna”
Kakakin Fadar Shugaban Kasar Rasha, Dmitriy Peskov ya bayyana cewa “Shugaba Putin na Rasha da Shugaba Erdogan na da alaka ta musamman.
Peskov ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai inda yace “hakika an gina wannan alakar ne bisa amincewa da juna, mutunta juna da kuma jajircewa wajen sauke nauyin da suka dauka.”