Sunak na iya maye gurbin Truss a matsayin sabon Firaiministan Birtaniya.
Tsohon ministan kudin Birtaniya, Rishi Sunak ne kan gaba a yunkurin zama sabon Firaiministan Birtaniya, bayan da Boris Johnson ya janye daga kokarinsa na koma wa kan kujerar.
A yanzu Penny Mardaunt ce kadai ta rage a cikin masu hamayya da Sunak a takarar shugabancin jam’iyyar Conservative.
Tsohon Firaiminista, Boris Johnson ya janye daga takarar duk da cewa ya ce ya samu adadin ‘yan majalisar da za su mara masa baya domin shiga takarar sake neman kujerar da ya bari a makonni da suka wuce.
Tun bayan da Liz Truss ta yi murabus kwanaki 45 da hawa kujerar Firaiminista a kasar, shi ne aka soma yunkuri na maye gurbinta. Abin da ke nufi kasar za ta samu shugaba na uku a cikin wannan shekarar.
Tsarin zaban sabon shugaba shine.
Da farko dan takara na bukatar ‘yan majalisa akalla 100 daga cikin ‘yan majalisa 357 na jam’iyyar Conservative su goyi bayansa.
Hakan na nufin cewa mutum biyu ne kadai za su iya shiga takarar.
dan har mutum daya ne kacal ya samu wannan adadin, to shi zai zama sabon firaiminista ba tare da hamayya ba.