An yabawa gwamnatin jihar Kano dangane da yunkurin gyara titinan jihar da ruwan sama ya lalata da cewa abin a yaba ne. Mai rajin ci gaban alummar rimin kebe dake jihar nan Alhaji mamuda zangon kabo ne yayi wannan yabon a zantawarta da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Mamuda zangon kabo ya bayyana cewar wannan yunkurin yana da muhimmanci kwarai da gaske duba yadda lalacewar titinan ke haddasa cunkoson ababan hawa ta yadda zaka ga ababan hawa sun kwashe sama da soi biyu a jerin gwanon cunkoson kafin su samu hanya su wuce inda zasu.
A kwanan nan ne gwamnatin jihar Kano ta sanar tare da zayyana titina guda arbain da biyu dake fadin jihar nan da zata gyara wanda yanzu haka ayyukan titinan sun fara gudana a wasu sassa daban daban na jihar.
Zangon kabo ya yabawa gwamnatin jihar Kano dangane da amsa kiraye kirayen jamaa kan lalacewar titinan Wanda hakan ta sanya gwamnati ta saurara har tayi yunkurin magance Matsalar inda yace wannan ya nuna cewa gwamnati har yanzu tana tare da jamaarta.
Daganan sai yayi kira ga alummar yankunan da gyaran titinan ya shafa kan cewar su baiwa gwamnati hadin kai wajen ganin aikin ya gudana cikin nasara tare da shawartar su kan su rika bada gudunmowarsu wajen yashe magudanan ruwansu kasancewar su ne Zasu amfana ba gwamnati ba.
Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa kaddamar da kasuwar dan gwauro dake karamar hukumar Kumbotso jihar nan musamman ma bangaren masu sayar da magunguna ta hanyar saukaka musu wajen killace magunguna kafin a kawo su shaguna domin sayarwa.
Daga karshe ya shawarci yan kasuwa kan su cigaba da tsarkake sanaar su da kuma tsare mutuncinsu tare da baiwa jamaa hadin kai wajen say are da ingantattun magunguna a kasuwanninsu.