Daga Walid Hari.
Aston Villa na nuna sha’awa kan tsohon shugaban kungiyar Tottenham da PSG Mauricio Pochettino a matsayin wanda ka iya maye gurbin Steven Gerrard. (Telegraph – subscription required)
Dan wasan tsakiya na Faransa N’Golo Kante bai kai ga kulla yarjejeniya da Chelsea ba sannan akwai rahotannin da ke cewa dan wasan mai shekara 31 na iya tafiya a matsayin wanda ba shi da kungiya a bazara mai zuwa. (Fabrizio Romano)
Joao Felix, 22, da Manchester United ke hange na tsaka mai wuya tsakaninsa da Atletico Madrid , sannan yayin da ƙungiyar ta Spaniya ke jaddada cewa ɗan wasan gaban na Portugal ba na sayarwa bane, wakilinsa Jorge Mendes yana duba wani zabin a 2023. (Here We Go podcast)
Wakilin dan wasan Napoli Victor Osimhen, wanda ake dangantawa da Manchester United da Arsenal, ya ce dan wasan Najeriyar ba shi da niyyar barin kungiyar ta Serie A. (Goal)
Brentford ta soma tattaunawa da shugaba Thomas Frank kan wata sabuwar yarjejeniyar sabuwar kwantaragi.
CBN ya soma gudanar da rangadi domin hukunta Bankuna da basa bayar da tsofaffin takardun kuɗi ga alumma
Daga kabiru A Dukawa Babban bankin Najeriya CBN ya ci alwashin hukunta duk wani bankin yan kasuwa da ya samu...
Read more