DCP Abba Kyari ya mika bukatar kotu tayi watsi da laifukan da NDLEA ke tuhumarsa da su

Dakataccen shugaban rundunar IRT, DCP Abba Kyari ya mika bukatar kotu tayi watsi da laifukan da NDLEA ke tuhumarsa da su baki daya.
Daga Walid Hari.
A kokarin dakatar da gurfanarsa a gaban kotu kan zargin safarar miyagun kwayoyi, dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, ya mika bukata a gaban kotu kan tayi watsi da zargin laifukan da Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA take masa.
Tsohon kwamandan rundunar IRT sun yayi ikirarin cewa bai dace a cigaba da zaman kotun ba saboda ba a gurfanar da shi a kwamitin ladabtarwa ba hukumar ‘yan sandan Najeriya ba kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.
Kyari, DCP Sunday Ubuha, ASP Bawa James da Sifetoci Simon Agirigba da John Nuhu a halin yanzu ana shari’arsu kan zargin laifuka biyar na safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar Punch ta gano cewa, Hukumar NDLEA zata soki bukatar wacce aka saka ranar Laraba domin saurarenta. Tun farko Kyari ya mika bukatar belinsa wanda kotun ta ki amincewa da ita saboda rashin isassun takardu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments