Shehin malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad ya bayyana dalilan da zasu sa ya kadawa kuri’ar say ga Dantakara shugaban kasa na yankin Iyamurai wato Peter Obi.
Gumi ya bayyana hakan ne a hirar da suka yi da Obi tare da tambayoyin da yayi masa kan tattalin arziki, ‘yan aware da sauran matsalolin kasar nan
’Dan takarar jam’iyyar LP na kujerar shugabancin kasa, Peter Obi ya kai ziyara wurin babban malamin kafin fara taron da wasu kungiyoyin arewa suka nemi yi dashi.
Fitaccen malamin dake zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya tarbi ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar Labour Party da mataimakinsa, Datti Baba-Ahmad a gidansa dake Kaduna.