Daraktan Shakhtar Donetsk Carlo Nicolini ya ce Arsenal da Manchester City na sahun gaba cikin kungiyoyin da suka nuna sha’awar daukar dan wasan Ukraine mai shekaru 21 Mykhaylo Mudryk, wanda aka sanya farashinsa kan sama da yuro miliyan 100, kamar dai kudin da Manchester United ta biya lokacin daukar dan wasan gaba na Ajax da Brazil Antony. (Calciomercato.it, via Mirror)
Newcastle United ta shirya tsaf domin yin tayin sayan dan wasan Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 28, a sabon kwantiragi, bayan kokarin da ya ke yi karkashin koyarwar manajansa Eddie Howe. (Telegraph)
Dan wasan tsakiya na Denmark Pierre-Emile Hojbjerg na cikin jerin wadanda za a bai wa kwantiragi a kungiyar Tottenham inda suke nuna sha’awar fara sabon lale da dan wasan mai shekara 27.(Times – subscription required)
Sporting Lisbon da ta kafawa dan wasan gaba Marcus Edwards kahon zuka, mai shekara 23, ta ce matakin mai da shi Portugal abu ne mai kyau a gare shi, amma zai so komawa buga wasa a kulub din sa Ingila. (Evening Standard)
Manajan Atletico Madrid Diego Simeone, mai shekara 52, ya kafe ba zai juya wa La Liga baya, duk da shan kayen da suka yi a Champions League. (Mail)
Fulham ta sake yin tayi a karo na biyu, domin daukar dan wasan tsakiya na Brazil Pablo Mai dan shekara 20, da dan wsan tsakiya na Sao Paulo Rodrigo Nestor, Maia, shekara 22, da dan wasan baya Igor Gomes, mai shekara 23, har da dan wasan baya Luizao, mai shekara 20. (HITC)
Ita ma Nottingham Forest ta nuna sha’awar daukar Maia, a shirye ta ke ta biya fam miliyan 9 domin matashin dan wasan na Brazil. (Nottinghamshire Live)
Manchester United na Nazari kan mai tsaron ragar Portugal Diogo Costa, mai shekara 23, ya yin da mai tsaron ragar Athletic Bilbao Unai Simon, mai shekara 25, inda suke duba yiwuwar karawa dan Sifaniya David de Gea mai shekara 31 kwantiragi (Athletic)
Southampton da Leicester City na bibiyar dan wasan kungiyar Toulouse da Moroko Zakaria Aboukhlal, mai shekara 22. Ana sa ran dan wasan zai buga gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Qatar a watan Nuwamba. (Southern Daily Echo)
Za a karawa sabon kocin Aston Villa Unai Emery kudade domin samun damar musanyar ‘yan wasa a watan Janairun badi. (Football Insider)