Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gida bayan balaguron aiki na kwana uku a Koriya ta Kudu kan harkokin lafiya na duniya.
A ranar Lahadi Buhari ya tafi Koriya tare da tawagar ministoci da shugabannin ma’aikatun ƙasar.
Shugaban ya shafe kwana uku yayin taron da aka yi laƙabi da ‘Makomar Rigakafi da Lafiyar Rai’. Yayin taron, Najeriya ta ƙulla yarjejeniya da wasu kamfanonin Koriya, ciki har da ta gyara matatar mai ta Kaduna.