Manchester City na fargabar Ilkay Gundogan zai bar kungiyar a kakar wasa mai zuwa. Har yanzu dan wasan wanda dan kasar Jamus ne mai shekara 32 bai amince ya sanya hannu a sabuwar kwantiragi ba. (Football Insider)
Manchester United na shirin tsawaita zaman Marcus Rashford a Old Trafford kafin karshen wannan shekarar domin hana wasu kungiyoyin yin gaba da shi. Dan wasan dan kasar Ingila mai shekara 25 na da damar tattaunawa da wasu kungiyoyin da zarar an kai watan Janairun badi. (Daily Mail)
Akwai rahoton da ke cewa Arsenal ta aika da wakilanta su kalli wasan Danilo, dan wasan tsakiya na kungiyar Palmeiras da kasar Brazil, inda ake cewa Gunners na sha’awar sayen dan wasan mai shekara 21 nan da watan Janairu. (Sun)
Akwai kuma rahoton da ke cewa Arsenal za ta dauko Facundo Torres, dan wasa mai shekara 22 dan Uruguay daga Orlando City ta Amurka. (Evening Sta ndard)
Chelsea kuwa na duba yiwuwar sayo Nelson Semedo, dan wasan baya na Wolves da Portugal mai shekara 28 domin ya maye gurbin Reese James dan wasansu mai shekara 22 da ya sami rauni. (Express)
Kocin Brighton Roberto de Zerbi ya zaƙu domin ya sayo Mykola Matviyenko, dan wasan baya na Uraine mai shekara 26, wanda kuma Shakhtar Donetsk ta saka wa farashin fam miliyan 17.2. (Athletic – subscription required)
West Ham na sa ido kan Isaiah Jones dan wasan baya na Middlesborough mai shekara 23 kuma dan kasar Ingila. (GiveMeSport)
Arsenal ta yi wa dan wasanta na baya William Saliba dan kasar Faransa mai shekara 21, sabon kwantiragi. (Athletic – subscription required)
Leicester ba ta damu ba kan batun sayar da Youri Tielemans a watan Janairu mai zuwa duk da rahotannin da ke cewa Arsenal na ci gaba da nuna sha’awa kan dan wasan dan Belgium mai shekara 25. (90min)