Shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta na son mayar da Lionel Messi Sfaniya a watan Janairu, sai dai duk wani yunkurin cimma wannan burin – na sada dan wasan dan kasar Argentina mai shekara 35 da tsohuwar kungiyarsa -zai fuskanci wasu manyan kalubala nan gaba. (Sport)
Messi zai yanke hukunci kan makomarsa bayan gasar cin kofin duniya a Qatar, kuma ba zai bar kungiyar PSG ba a watan Janairu ko da ba ya son tsawaita zamansa da kungiyar ta kasar Faransa. (Ben Jacobs)
Sporting Lisbon a shirye ta ke ta yi wa Manchester United tayi domin raba ta da Cristiano Ronaldo, mai shekara 37 da haihuwa a karo na biyu. (Sunday Mirror)
Kwanitiragin dan wasan tsakiya na Chelsea N’Golo Kante za ta kare a karshen kakar wasa badi kuma dan wasan mai shekara 31 wanda dan kasar Faransa ne na cikin jerin ‘yan wasan da Barcelona ke hari yayin da ta ke neman wanda zai maye gurbin Sergio Busquets mai shekara 34 da haihuwa. (Relevo – in Spanish)
Barcelona na fatan sayar da Memphis Depay a watan Janairu mai zuwa, inda kungiyar Juventus ta Italiya ta bayyana sha’awarta ta saye dan wasa mai shekara 28. (Sport)
Dan wasan tsakiya na Ivory Coast Franck Kesie mai shekata 25 ba ya jin dadin yadda ake benca shi a Barcelona kuma ya bukaci a ba shi damar komawa gasar Serie A ta Italiya. (Fichajes – in Spanish)
Manchester City na shirin yi wa Bernardo Silva, dan wasanta mai shekara 28 sabon tayi mai gwabi na tsawaita zamansa har na tsawon shekara biyar. (Football Insider)
Brighton da Everton na rige-rigen sayen Caio Henrique, dan Brazil kuma dan wasan baya na kungiyar Monaco ta Faransa mai shekara 25. (IG Esporte – in Portuguese)
Tsohon kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce har yanzu bai yanke hukunci kan lokacin da zai koma bakin aikinsa na horas da wata kungiyar kwallon kafa ba. (Sp ortstar)