Paris St-Germain na son tsawaita kwantiragin Lionel Messi zuwa kaka daya. Yarjejeniyar dan wasan mai shekara 35 za ta kare a karshen Yunin 2023. (Le Parisien – in French, subscription required)
Bayern Munich na tsara yadda za ta dauki dan wasan Manchester City, mai shekara 32, Ilkay Gundogan a kakar badi. (90min)
Barcelona na tattaunawa kan yadda za ta sayi dan wasan Portugal, Ruben Neves, mai shekara 25 daga Wolves, wadda ke fatan kammala cinikin a Janairun 2023.
Kociyan Sporting Lisbon, Ruben Amorim ya ce mafarkin kowa a kungiyar shi ne Cristiano Ronaldo ya sake koma mata taka leda, to sai dai ya ce ba su da kudin da za su iya biyan albashin dan kwallon. (Football.London)
Ronaldo yana da zabin barin United ya koma taka leda a gasar kwallon kafa ta Amurka ta Major League Soccer, watakila a Inter Miami ko LA Galaxy ko kuma LAFC. (Los Angeles Times)
Arsenal za ta iya musaya da Albert Sambi Lokonga, mai shekara 23, domin a sayar mata da mai taka leda a Lazio, Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27. (Calciomercato – in Italian)
A shirye Chelsea take ta fara batun tsawaita zaman Mateo Kovacic, mai shekara 28, bayan gasar kofin duniya. Yarjejeniyarsa za ta kare kasa da kaka biyu a kungiyar Stamford Bridge.
Watakila dan wasan Ingila, Jude Bellingham, mai shekara 19, ya yanke shawarar ci gaba da taka keda a Borussia Dortmund a badi, duk da cewar Liverpool da Real Madrid na son daukar dan kwallon. (Sky Sports, via Express)
Dan wasan Lille, mai shekara 22, Jonathan David ya ce dama na nan tafe nan gaba da zai buga tamaula a babbar kungiya. Ana ta alakanta dan kwallon Canada da cewar watakila zai koma Chelsea ko Arsenal ko kuma Manchester United. ( Mirror)