Najeriya zata amfana da sama da Dollar Amurka miliyan dubu daya da miliyan dari takwas (1.8 billion dollars) domin bunkasar harkokin kasuwanci.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa, bankin cigaban bankunan musulunci na duniya na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin noma a fadin duniya.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin Shugaban cigaban Bankin Musulunci na duniya Dakta Muhammad Sulaiman Al-Jaseer yayin da ya ziyarce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce, bankin na taimakawa manoma musamman a nan jihar Kano duba da tarihin da jihar kano take dashi a kasuwanci da noma.
Ya kuma yabawa bankin domin gina wata cibiya a karamar hukumar Gwale.
A nasa jawabin shugaban bankin musulunci na duniya Muhammad Sulaiman Jasi yace, bankin bunkasa cigaban bakunan musulunci zai kashewa Nigeria sama da 1.8 billiyan dolas domin munkasa harkokin kasuwanci.
Shugaban Bankin Musuluncin yana tare da mataimakinsa Dakta Mansur Mukhtar adnan.
Daga sakataren yada labarai na masarautar kano Abubakar balarabe kofar na’isa