Kasar Uganda: Mutane 63 sun kwanta dama bayan da adadi mai yawa ke kwance a Asibiti sanadiyar cutar Ebola

Ma’aikatar lafiya ta kasar Uganda ta tabbatar da karuwar alkaluman wadanda cutar Ebola ta kashe a kasar zuwa mutum 63, yayinda ake da tarin mutanen da ke kwance a cibiyar kula da masu cutar ake ci gaba da basu kulawa.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus da ke bayyana hakan a jawabinsa kan halin da ake ciki a Uganda, ya ce Ebolar wadda ta zama annoba kawo yanzu ta fantsama a sassan kasar.

Kawo yanzu dai akwai samfuran cutar har guda 6 da suka bulla a kasar, sai dai wadda ake yiwa lakabi da Sudan Ebolavirus tafi yaduwa da illa, lura da cewa har kawo yanzu babu rigakafinta.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa kawo yanzu jami’an lafiya 10 suka kamu da cutar inda 4 daga cikinsu suka mutu, yayinda wasu karin 4 da suka fara samun sauki.

A wani karin bayaninta ministar lafiyar kasar ta gabashin Africa Jane Ruth Aceng Ocero ta ce cikin jami’an lafiya da suka mutu har da wani dan Tanzania da ya je kasar aiki amma ya kamu da cutar.

Kawo yanzu dai akwai samfuran allurar rigakafin cutar samfurin Sudan sai dai har yanzu ba a gama aikin gwaji da tantance su ba, abinda ya zama tilas kafin bada umarnin fara gwajin su kan dan adam.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments