Jami’an Kenya sun sanar da cewa ba a samu man fetur da iskar gas a gabar tekun kasar ba, lamarin da ya janyo rikicin diflomasiyya da makwabciyarta Somaliya.
Hukumar Kula da Makamashi da Man Fetur ta Kenya ta sanar da kawo karshen binciken albarkatun kasa a yankin da aka fi sani da rijiyar Mlima-1 a tsibirin Lamu.
An yi zaton cewa akwai man fetur a yankin da ya haddasa rikici na tsawon shekaru kusan 10, kamar yadda Kenya da Somaliya ke ikirari a kai.
A karshe, jirgin ruwan da ke hakar mai na kamfanin Italiya, Eni ya kasa samun albarkatu a yankin L11B a tsibirin Lamu, duk da aikin da aka kwashe watanni ana yi.
Kenya da Somaliya dai sun dade suna takun saka a gabar tekun da ke kallon Tekun Indiya, wadanda ake ikirarin suna da arzikin mai da iskar gas.
A shekarar da ta gabata ne kotun kasa da kasa ta yanke hukuncin kan iyakar tekun da ya haifar da cece-kuce a tsakanin kasashen biyu bisa ka’idar adalci da daidaito, inda aka bar galibin yankin da ake takaddama a kai zuwa Somaliya, kadan kuma ga Kenya.