Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, ya mika ta’aziyyarsa ga shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido da budurwarsa, Chioma Rowland kan mutuwar dansu, Ifeanyi. Ifeanyi dai ya nitse a cikin rafin wanka na shakatawa dake cikin gidansa dake unguwar Banana Island dake jihar Legas a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba.
Da yake martani a kan wannan mummunan al’amari da ya samu masoyan biyu a shafinsa na Twitter, Kwankwaso ya roki Allah da ya yiwa Davido da Chioma jagora a wannan mawuyacin lokaci. Kwankwaso ya ce: “Allah yayi maku jagora sannan ya fitar da ku daga wannan lokaci nab akin ciki. – RMK.
Bashir ya rubuta: “Tunanina da addu’o’ina na tare da @Davido, wanda ya rasa dansa, Ifeanyi. Kada Allah yasa kowasu iyaye su dandani radadin rashin da ta irin wannan mummunan al’amari.
A gefe guda, mun ji cewa yan sanda sun kama dukkanin ma’aikatan gidan shahararren mawakin Najeriya, Davido kan mutuwar dansa, Ifeanyi. Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da cewar dukkanin ma’aikatan na tsare a hannunsu don amsa tambayoyi.