Biyo Bayan Korafe Korafe, Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa wani Kwamitin wucin gadi mai dauke da mutum 7 da zai gudanar da bincike akan yadda aka kasafta Naira biliyan 500 ga shiyoyi shida na kasar daga bankin raya kasa na Najeriya.
Kafa Kwamitin binciken ya biyo bayan wani kudurin zargin badakala ne da Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya kawo zauren Majalisar Dattawan, to saidai wasu Sanatocin na ganin binciken ba zai yi wani tasiri ba.
A cikin jawabinsa ga Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce rahoton da Bankin Raya Kasa ya fitar a ranar 13 ga watan Yuli na wannan shekara da muke ciki, ya bayyana yadda aka kasafta Naira biliyan 483 a matsayin lamuni da ya kamata a tallafa wa kananan masana’antu domin ceto su daga rugujewa.
Ndume ya ce abin da ya daga masa hankali shi ne cewa kashi 11 cikin 100 na Kudin ne aka ware wa jihohi 19 na Arewa, wanda ya kama Naira biliyan 53 da miliyan 130 kacal, amma Jihar Lagos ta samu kashi 47 cikin 100, wanda ya kama Naira biliyan 227 da miliyan 10 ita kadai.