Kungiyoyin yankasuwa na cigaba da kiraye kirayen babban bankin kasarnan daya kara waadin da ya sanya na 31ga watan janairun wannan shekarar domin daina karbar tsoffin kudade a bankunan kasarnan.
Shugaban matasan yan kasuwar singa Alhaji Aminu mai kurkura wanda lawan Dan hajiya mai rice ya jagoranta ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar.
Lawan Dan hajiya yace yan kasuwa na cikin kalubale dangane da wannan waadin da gwamnati ta sanya na dakatar da karbar tsofaffin kudade wajen gudanar da hada hadar kasuwacinsu na yau da kullum.
Ya bukaci gwamnatin ta sake yin duba na tsanaki domin kara lokaci musamman saboda alummar karkara da suke shigowa cikin garin domin siyayyar kayayyakin da suke kasuwacinsu.
Ya kuma jaddada cewar yanzu haka wadansu guraren sun dakatar da karbar tsoffin kudade domin kaucewa gudun tafka asara, amma akwai bukatar yin duba na tsanaki a kan kananan yankasuwa da suke bukatar su samu damar shigar da kudadensu.
A jawabinsa Sakataren kungiyar kasuwar singa dake gidan Abdurrashid mai turare Alhaji Auwalu Ahmed rijiyar lemo yace da yawa wasu bankunan idan kaje babu sabbin kudaden wanda kamata yayi kudaden su wadata a bankunan wannan shi zai sanya a samu yawaitar sabbin kudaden a hannun alumma musamman yan kasuwa.
Kazalika Auwalu rijiyar lemo ya shawarci yan kasuwa musamman kanana dasu rika baiwa masu sanaar P. O. S domin tura musu kudadensu zuwa asusunsu da zarar sun kammala kasuwacinsu a ranar, har zuwa nan da lokacin da gwamnati ta sanya waadin dakatar da karbar tsoffin kudaden.