Kasar China ce ke rike Da ragamar tattalin arzikin Duniya : Ngozi Okonjo-Iweala

Darakta Janar ta kungiyar kula da harkokin cinikayya ta duniya WTO, Ngozi Okonjo Iweala, ta ce taron dandalin tattalin arzikin duniya ya tunatar da kasa da kasa cewa, ya kamata a yi hadin gwiwar da ba a taba yin irinsa ba, domin tabbatar da warware matsalolin dake tarnaki ga ci gaban duniya.

Ngozi Okonjo Iweala ta bayyana haka ne yayin da take zantawa da wakilin CMG, bayan taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya da aka yi a Davos.

Darakta Janar din ta kara da cewa, duniya bata gama farfadowa daga mummunan tasirin annobar COVID-19 ba, amma yanayin na ingantuwa. Tana mai cewa, sake bude kofofin kasar Sin wani kyakkyawan batu ne ga duniya.

A cewarta, “da farkon fari, kasar Sin za ta samar da bukatun kayayyaki a cikin gida, kuma bangaren samar da kayayyaki zai koma yadda yake, don haka, wannan wani abu ne mai kyau ga duniya. Kasar Sin ita ce kashin bayan ci gaban duniya, kuma sake bude kasar, abu ne mai kyau.”

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments