China ta zargi manufar Daidaita kudi na asusun ajiyar Amurka ya kawo matsin lamba ga tattalin arzikin kasar Argentina.
Shima shugaban kasar Argentina Alberto Fernández ya bayyana cewa a wannan yanayin da ake fuskantar sarkakiyar sauye-sauyen kasa da kasa bi kamata kasar Amurka ta nuna tsagwaron son zuciyar ta ba
A zantawar sa da jaridar CMG yace yayi matukar amincewa da shawarar ci gaba da ta tsaro da shugaban kasar China Xi Jinping ya gabatar masa
Fernández ya ce, “A gani na, manufa mafi muhimmanci da kasar Sin ta gabatar ita ce girmama ra’ayin bangarori da dama, kuma muna goyon bayan irin ra’ayin. Ina adawa da nuna danniya ko babakere, kuma ba na son wata kasar dake nuna babakere ta wanzu a duniya. Shawarar da shugaba Xi ya gabatar, yana da nufin inganta ra’ayin kasancewar bangarori da dama da mutunta mulkin kai da hali na musamman na kowace kasa.
Ya ce yaduwar annobar ta nuna rashin daidaito wajen ci gaban tattalin arzikin duniya. Lokacin da aka fara samar da alluran rigakafin COVID-19, an ba da kashi 90 cikin 100 na alluran duniya ga al’ummar da yawansu ya kai kashi 10% na duniya, wanda ke nuna rashin adalcin tsarin duniya. Kasashen Rasha da Sin sun kawo mana agaji da alluran rigakafi. Na yi imanin cewa, a duniyarmu ya kamata mutane su mutunta juna kuma kowa ya iya samun muhimman abubuwan da suke bukata kamar allurar rigakafi a yayin da ake tinkarar annoba