A wani raho da kungiyar yan fansho ta karamar Hukumar Kura ta aiko wa da Aksam Media tace yan kungiyar na karamar Hukumar basu amince da matakin da uwar kungiyar ta jiha take kokarin dauka ba.
Daga Dantala Uba Nuhu Kura
A cewar shugaban yan fansho na karamar Hukumar ta Kura an turo shine daga jagorancin kungiyar na jiha karkashin jagorancin Salisu Ahmad Gwale domin yaji ta bakin sauran yan fanshon karamar Hukumar bisa matakin da suke son dauka na kin karbar kudin watan Satumba in har gwamnati ya kara yankar musu.
Sai dai a jawabin nasa yace yan kungiyar a matakin karamar Hukumar ta Kura basu amince da yin zanga-zanga ko kuma kin karbar kudin ba.
Amma suna rokon majalisar jiha tasa gwamna ko bashi ne ya ciyo domin a biya su kudaden su na sallamar aiki.
Ya kara da cewa a karamar Hukumar Kura suna da yan fansho wajan mutane 500 wadanda suke jiran kudin sallamar aiki a matakin jiha da na karamar Hukuma.