Luca Modric ya buga wa Real Madrid wasa na 300 a La Liga.
Daga Filin wasannin Aksam Media.
Ranar Lahadi Real Madrid ta je ta doke Atletico Madrid da ci 2-1 a wasan hamayya a gasar La Liga fafatawar mako na shida.
Wasa na 300 kenan da Luka Modric ya yi wa Real Madrid a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Dan kwallon tawagar Croatia na buga kaka ta 11 a Santiago Bernabeu, wanda aka ci wasa 204 da shi, ya kuma zura kwallo 23 jumulla.
Haka kuma Modric ya lashe kofin La Liga uku a Real Madrid.
Modric ya buga wasa da yawa a La Liga a kakar 2020/21 da yin fafatawa 35, sai kakar 2013/14 da ya yi karawa 34.
Kungiyar da ya fuskanta da yawa ita ce Atletico Madrid har karo 20, kungiyar da ta yi rashin nasara da yawa a wasan da ya buga wa Real, ita ce Celta Vigo sau 13.