Gwamnatin Jihar Anambra ta haramta Amfani da gajerun yan tofi ga dalibai a fadin jihar.
Kwamishiyar Ilimi ta Jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ce ta bayyana hakan a Awka inda tace haramcin ya zama dole domin makarantu za su dawo hutu a ranar Litinin
Kwamishinan ta yi tir da sabon yayin da ake yi na saka mini siket a matsayin kayan makaanta kuma ta ce rashin tarbiya ne kuma ba za a amince yan makaranta su rika yin hakan ba.
Ta ce: “A matsayin dalibai ya kamata ka yi shiga tsaf-tsaf, ta nuna halaye masu kyau ba shiga irin ta rashin tarbiya ba yayin zuwa makaranta.
Ta kara da cewa abin da aka amince shine tsawon unifom ya rufe gwiwa ba ya gaza kai wa gwiwa ba, wanda shine sabon yayin da ke bazuwa a makarantu.”