Kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi ta kasa, ta yi Kira ga yankungiyar musamman masu Kai dabbobi kudancin kasarnan, da su kaucewa yin lodin dabbobin da ya wuce kima domin kaucewa yawan Asara da cin mutunci da ake yiwa masu fataucin shanu da dabbobi a kudancin kasarnan.
Shugaban kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi na kasa Alh mustapha Ali ne ya yi wannan kiran a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Yace kuginyar tana iya kokarinta domin kare mutuncin yankungiyar a kodayaushe kuma a koina suke ciki kasar nan, musamman kudancin kasarnan da ake yiwa yan kungiyar cin
Kishin da aka ga dama.
Mustapha Ali, Ya shawarci Gwamnatin tarayya data jihohi da su shiga lamarin wannan kungiya duba da yadda ake kashe mata alummarta da suke fataucin shanu da dabbobi zuwa kudancin kasarnan, Saboda yankunan kudu suna daukar matakin da suka ga dama wajen musgunawa masu fataucin shanu da dabbobi.
Ya kamata yayi Gwamnonin Arewacin kasarnan su zama masu kishin yankunan su, ta hanyar Samar da hanyoyin da za su hana faduwar abubuwan da suke faruwa akan yankungiyar da suke fafutikar shigar da kayayyakin masarufi ciki har Kai shanu da dabbobi
Zuwa kudancin kasarnan.
Shugaban kungiyar yace muddin gwamnati ba ta dauki matakan dakatar da wannan cin zarafi da ake yiwa yankungiyar Ba, to za su dakatar da Kai dabbobi zuwa kudancin Najeriya, kasancewar anan ne kawai suka fi samun matsala kisan gillar da ake yiwa yankungiyar basu ji ba, Basu gani ba.
Daga karshe Shugaban kungiyar yayi kira ga yankungiyar da sauran alummar kasarnan da suke Kai dabbobi da shanu zuwa yankunan kudancin kasarnan, da su ci gaba da hakuri domin kuwa, kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi tana nan tana kokarin ganin ta daidaita alamura domin kare lafiyarsu da dukiyoyinsu da ma rayukansu a duk inda Zasu shiga a fadin kasarnan.