Hukumar kididdiga ta kasa ta magantu a kan hauhawar kayayyakin masarufi

Hukumar Kididdiga ta kasa ta fitar da jadawalin  da ke nuni da cewa, hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan  ya karu zuwa kashi 19.64% lamarin da ke zama mafi girma da muni da aka taba samu a Najeriya  tun shekarar 2005 .

Wannan dai na nuni da cewa matsin rayuwa da al’ummar kasar nan ke fuskanta ya dada muni la’akari da canjin da aka samu na hauhawar farashin kayayyaki musamman na masarufi wanda suka rubanya na shekarun baya da suka gabata

An samu kari a hauhawar farashin kayayyakin abinci, daga kashi 20.60 cikin 100 a watan Yuni zuwa kashi 22.02 a watan Yuli, wanda ake ganin ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin biredi da hatsi, da sauran kayayyakin abinci

Alkalumar farashin kayayyakin masarufi na hukumar kiddiga ta kasa a watan yulin da ya gabata  ya yi nuni da cewa an samu karuwar kashi 18.17 cikin 100 wato sama da kashi 18.62 cikin 100 da aka samu a watan Yuni da ya gabata a shekarar lamarin da ke nuni da cewa an samu sauyin farashi a ayyuka da kayyakin da mutane ke amfani da su na yau da kullun batun da masanin tattalin arzikin kasa a Najeriya Dakta Isa Abdullahi ya ce hakan ba karamin shafar tattalin arzikin kasar zai yi ba, ta fannin tsare tsare.

A nashi bangaren, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a kasar Hassan Sardauna cewa ya yi dole al’umma su yi wa kasar adalci domin hauhawar farashin kayayyaki ya shafi kasashe da dama a fadin duniya.

Rahoton dai ya bayyana cewa an samu kari mai yawa a farashin kudin siyan iskar gas, man fetir da dizal da jigilar fasinjojin jiragen sama, tufafi, da dai sauransu

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments