Hukumar NIMET ta bayyana cewa Jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi, Yobe, Borno, Taraba da Adamawa zasu Iya fuskantar Ruwa da matsananciyar tsawa na tsawan kwanaki uku daga safiyar yau Jumma’a 19-08-2022
Rahoton da hukumar ta kula da yanayin sararin samaniya ta kasa ta fitar a yammacin Jiya alhamis shine ya tabbatar da hakan.
Kazalika tace yana zai Iya game jihohin Jigawa, Sokoto, Kaduna, Bauchi, Gombe, Zamfara, Kano, Katsina, Borno, Yobe da kuma Kebbi.
Ta kara da cewa yanayin ka Iya hadawa da yankin Arewa ta tsakiya inda jihohin Kwara, Niger da Abuja zasu Iya fuskantar Ruwa mai tsanani.
Haka yanayin zai kasance a jihohin Arewa ta tsakiya wato Abuja Benue, Kogi, Plateau da Nasarawa
Daga kudancin Kasar nan kuwa A safiyar yau Jumma’a jihohin Rivers da Akwa Ibom ruwa zasu samu jifajifa
Sai kuma Ekiti, Ondo, Ogun, Oyo, Osun, Enugu, Imo, da Edo zasu Fiskaci yanayin Ruwa sama-sama