Kungiyar Manyan Malaman Musulmai ta Duniya ta yi kira ga kasashen Musulmai da su kawo agajin gaggawa ga yankunan da girgizar kasa ta afku.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Kungiyar Manyan Malaman Musulmai ta Duniya ta fitar, an bayyana cewa, kungiyar tana mika gaisuwarta ga al’ummar Turkiye da Siriya sakamakon girgizar kasar da ta shafi yankin Kahramanmaras da kuma kasashen yankin.
A cikin sanarwar na fatan rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu a girgizar kasar da kuma samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata, an yi kira ga kasashen Musulmai da kungiyoyin ba da agaji da su kai agajin gaggawa a yankunan da girgizar kasar ta afku.
Haka zalika Qatar ta kaddamar da wani shirin bada agaji ga wadanda girgizar kasa mai karfin awo 7.7 ta shafa a Kahramanmaras.
A wata rubutacciyar sanarwa da Kungiyar ba da agaji ta Qatar ta fitar, an bayyana cewa an kaddamar da wani gangamin agaji ga Turkiye da Siriya mai taken “taimako ga wadanda girgizar kasa ta shafa.”
A cikin sanarwar an bayyana cewa an shirya tallafin magunguna da kayayyakin jin kai tare da kokarin isar da suyankin.
A cikin sanarwar an gayyaci masu hannu da shuni don bayar da tasu gudummawar a yakin, an kuma yi kira da a hana halin da wadanda girgizar kasar ta shafa tabarbare.
A cikin sakon ta’aziyyar sa, babban sakataren Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai ta OIC, Hissein Brahim Taha ya bayyana cewa suna tare da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a girgizar kasar.
Taha ya yi kira ga kasashe mambobin OIC, da cibiyoyin da abun ya shafa, da dukkan kawayenta da su bayar da tasu gudummuwar a kokarin aiyukan ceto da ake gudanarwa a Turkiye.