Kasashen duniya da dama na kai taimako zuwa Türkiye
Sakamakon girgizar kasa masu karfin awo 7.7 da 7.6 da suka afku a gundumomin Pazarcik da Elbistan na birnin Kahramanmaras, kuma suka shafi larduna 10, kasashe da dama sun aike da tawagaoginsu domin ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzan gine-gine.
A cikin sanarwar da Ma’aikatar Agajin Gaggawa ta Kasar Azabaijan ta fitar, an sanar da cewa bisa umarnin Shugaba Ilham Aliyev, jirage 2 dauke da kayayyakin agaji za su tashi zuwa Türkiye nan da dan lokaci.
A cikin sanarwar an bayyana cewa daya daga cikin jiragen yana da cikakken asibitin wucin gadi.
Azabaijan ta aike da jami’ai 420 zuwa Türkiye don shiga aiyukan ceto.
Jiragen ruwa guda 2 dauke da magunguna, abinci, ababen dumama wuri, barguna, tufafi, tantuna da sauran kayayyaki da sassan sojoji, cibiyoyin gwamnati daban-daban da ‘yan kasar Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus (TRNC) suka bayar, sun tashi zuwa Türkiye.
A cikin sanarwar da Ofishin Shugaban Kasar Uzbekistan ya fitar, tare da umarnin Shugaban kasar Sevket Mirziyoyev, tawagar masu aikin ceto mai mutane 100 daga Ma’aikatar Agajin Gaggawa ta Uzbekistan, jirgin sama dauke da motoci na musamman da na’urori da kayayyakin agaji sun tashi daga filin jirgin saman Tashkent zuwa Türkiye domin shiga aiyukan ba da agaji ga wadanda suka jikkata a girgizar kasar.
Turkmenistan ta aike da tawagogin ceto da jiragen sama dauke da kayan agaji zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa.
Kasar Belarus ta sanar da cewa za ta aike da tawagar bincike da ceto zuwa kasar Türkiye domin tallafa wa mutanen da suka makale a karkashin baraguzan gine-gine bayan girgizar kasar da ta afku a Kahramanmaras.
Kasar Jojiya ta aika da tawagar bincike da ceto zuwa Türkiye domin ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzan gine-gine.
Kakakin Harkokin Wajen Amurka, Ned Price ya sanar da cewa a cikin kwanaki masu zuwa wasu tawagogi biyu na mutane 79 da za su shiga aikin ceto bayan girgizar kasar da ta afku a Kahramanmaras za su isa Türkiye, sannan kuma za su bayar da taimakon agaji ga Türkiye da Siriya.
Ofishin jakadancin Türkiye da ke Washington ya kuma fara aikin ba da agaji ga wadanda girgizar kasar ta shafa.
Kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyi daban-daban a Amurka suna gudanar da aiyukan ba da agaji ga wadanda girgizar kasar ta shafa.
Ana kuma jigilar kayan agajin da aka tattara a Turkevi da ke birnin New York zuwa yankin da bala’in ya afku.
Ministan Agajin Gaggawa na Rasha, Aleksandr Kurenkov ya sanar da cewa an aike da tawagogin bincike da ceto na kasar Rasha da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa a Türkiye.
Kasar Rasha ta kuma aike da asibitin wucin gadi domin kula da wadanda suka jikkata a girgizar kasar.
Faransa ta sanar da cewa tawagogin bincike da ceto na mutane 136 wadanda ta aike sakamakon girgizar kasar da ta afku a Kahramanmaras, sun tashi.
Tawagar jami’ai 41 da karnuka 7 sun tashi daga birnin Cologne na kasar Jamus don shiga aiyukan ceto.
Tawagar agajin gaggawa ta kasa da kasa mai mutane 18 da Japan ta aika zuwa Türkiye sakamakon girgizar kasar, ta isa birnin Istanbul.
Kasar China ta aike da tawagar fararen hula ‘yan taimako zuwa kasar Türkiye domin tallafawa kokarin ceto mutane bayan girgizar kasa da ta afku a Kahramanmaras.
Kasar Mekziko ta aika da tawagar bincike da ceto mai mutane 145 zuwa Türkiye bisa umarnin Shugaban kasar Andres Manuel Lopez Obrador.
Gwamnatin kasar Hungary ta aike da wata tawaga dauke da mutane 55 domin tallafawa aiyukan agaji na kasa da kasa a Türkiye sakamakon girgizar kasar da ta afku.
Pakistan ta aika da tawagar bincike da ceto zuwa Türkiye bisa umarnin Firaministan kasar, Shahbaz Sharif.
Shugaban El Salvador Nayib Bukele ya sanar da cewa zai aike da tawagar bincike da ceto zuwa Türkiye bayan girgizar kasar da ta afku.
Bayan girgizar kasar, Arewacin Macedonia ta yanke shawarar tura tawagar bincike da ceto mai mutane 40 zuwa Türkiye.
Firaministan Falasdinu, Muhammed Istiyya ya sanar da cewa za a aike da tawagogin jami’an tsaron fararen hula da likitoci domin shiga aiyukan ceto a kasashen Türkiye da Siriya bayan girgizar kasar da ta afku a Kahramanmaras.
Jimilar kasashe 14, 12 daga cikinsu kasashen Larabawa daga Gabas ta Tsakiya, sun sanar da cewa za su aike da tawagogin bincike, ceto da ba da agaji zuwa kasar Türkiye, domin dakile illolin girgizar kasa masu karfin awo 7.7 da 7.6 da suka afku a Kahramanmaras kuma suka shafi wasu larduna 10.