Kawo yanzu, girgizar kasa biyu masu karfin maki 7.8 da suka aukawa kasar Turkiya a jiya Litinin, sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 3000 a kasashen Turkiya da Syria dake makwabtaka da ita. Daga cikin mutanen da suka mutu, 2379 sun mutu ne a Turkiya, yayin da 711 suka mutu a Syria.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya sanar da zaman makoki na kwanaki 7, haka zalika ma’aikatar ilimi ta kasar, ta sanar da rufe dukkan makarantu na tsawon mako guda.
Nan da nan bayan aukuwar iftila’in, MDD ta kaddamar da ayyukan agaji domin kai dauki ga mutane da yankunan da lamarin ya shafa.
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana a jiyan cewa, yana bayar da cikakken goyon baya ga ayyukan agajin tare da nazarin bukatun da ake da su. Haka kuma, Achim Steiner, shugaban sashin raya yankuna na MDD, ya ce hukumarsa ta shirya taimakawa wadanda lamarin ya shafa.
Shi ma Tedros Adhanom Ghebreyesus, darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya ce an amince da tura wani ayarin jami’an lafiya tare da samar da hidimomin kiwon lafiya ga mutanen da suka jikkata da sauran masu rauni.