Shugabancin kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi ta kasa ya bukaci gwamnatin tarayya da babban bankin kasarnan kan su bari a rika amfani da tsoffin kudade har sabbin su wadata a hannun alumma ta yadda da tsoffin kudade sun shiga bankuna ba damar sake fitowa.
Shugaban kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi na kasa Alhaji Mustafa Ali ne ya sanar da hakan azantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Shugaban ya bayyana cewar idan gwamnatin tarayya da babban bankin kasarnan Zasu wadatar da kudaden a hannun alumma sai bankuna su rika yiwa tsoffin kudaden alama ta yadda ba Zasu sake fitowa daga bankuna ba.
Ya kuma bayyana cewar idan gwamntin tarayya da babban bankin kasarnan Zasu yi amfani da tsarin da kasar Amurka tayi kan sabuwar Dala da ta fito da ita wanda har yanzu ana amfani da Tsohuwar dalar ta yadda nan da wani lokaci zaa dai na ganin tsoffin dalolin sai dai sabbin a hannun alummarsu, to hakan zai ceci tattalin arzikin kasarnan daga samun nakasu
Mustafa Ali yace muddin gwamnati ba ta dauki irin wannan tsarin na kasar amurka ba to alummar kasarnan ba Zasu yi Sam barka da sauya fasalin kudi a fadin kasarnan ba.
Ya kuma koka kan cewar sama da kwanaki Ashirin kenan harkokin kasuwancinsu ya dakata sakamakon idan sun yi cinikin dabbobin ba wanda zai yadda ka tura masa kudi ta asusun bankinsa.
Don haka ya ke shawartar yayan kungiyarsu kan su tabbata sun mayar da tsoffin Kudadensu bankuna kafin nan da karshen waadin kwanaki goman da babban bankin kasarnan ya kara.