Shugabancin kungiyar kasuwar abinci ta duniya dake Dawanau a karamar hukumar dawakin tofa ta bayyana gamsuwar ta dangane da Karin kwanaki goma da babban bankin kasarnan yayi domin mayar da tsoffin kudade bankuna Don kada kananan yan kasuwa su tafka asara.
Sakataran kungiyar kuma Garkuwan matasan Arewacin kasarnan Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi ne ya sanar da hakan azantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Garkuwan ya godewa Allah tare da babban bankin kasarnan bisa wannan dama da ya baiwa yan kasuwa musamman kanana wadanda basu da asusun Ajiyar banki domin su samu damar shigar da kudadensu bankuna kafin waadin ya kare domin gudun tafka asara.
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da babban bankin kasarnan bisa yin wannan hange da suka yi wajen Karin waadin wanda ba don haka ba da wannan tsarin na baya ya karya yan kasuwa da dama musamman kananan yan kasuwa tare da durkushewar kasuwanci da tattalin arziki a fadin kasarnan.
Don haka yake kira ga yayan kungiyarsu na birni da na karkara kan su tabbata sun yi amfani da wannan Karin waadin da babban bankin kasarnan ya yi wajen mayar da tsoffin kudadensu bankuna kafin waadin ya kare domin gudun tafka asara.
Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi ya kuma yi Kira ga gwamnatin tarayya da babban bankin kasarnan kan yayi kokari wajen ninka kudaden da yake turawa kananan bankuna domin Kudaden su yawaita a hannun alumma
wanda ko da waadin da babban bankin kasarnan ya kara bazai illata alumma da kananan yan kasuwa ba.