Kungiyar EAC ta dauki gabarar sa santa yan tawayen kasar Congo da gwamnatin kasar

A jiya ne, ‘yan tawayen M23, suka mika sansanin soji na Rumangabo da suka kwace a yankin arewa maso gabashin kasar Congo Kinshasa a watan Oktoba ga sojojin kungiyar raya kasashen gabashin Afrika (EAC) a hukumance.

An gudanar da bikin mika sansanin soji mai tazarar kilomita 40 daga birnin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa ne, a gaban jami’an rundunar yankin EAC, da tawagar tabbatar da hadin gwiwa ta manyan tabkuna, da jagororin ‘yan tawayen M23.

Mataimakin kwamandan rundunar EAC mai kula da yankin, Emmanuel Kaputa, ya ce, bikin ya nuna ci gaba da gudanar da wani aiki da tuni aka fara aiwatarwa, kafin janyewar ‘yan tawayen daga garin Kibumba a watan Disambar 2022.

A ranar 23 ga watan Disamban shekarar 2022 ne, ‘yan tawayen suka janye daga Kibumba, kimanin kilomita 20 daga Goma, a matsayin ” nuna fatan alheri da aka yi da sunan samar da zaman lafiya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments