Fitaccen mawakin nan Aminudden Ladan Abubakar wanda aka sani da Alan Waka yace rashin tabbas ne yasa ya ajiye takarar sa kuma ya fice daga jam’iyyar ADP ta Sha’aban Sharada.
Alan waka ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 yau asabar
Yace dama gayyatar sa akai cikin jam’iyyar kuma akai masa alkawarin za’a bashi takarar dan takarar tarayya a karamar hukumar Nasarawa, amma bayan ya fara harkokin takarar gadan-gadan kuma hukumar zabe ta fitar da sunayen yan takara kuma ya ga babu sunan shi.
A sunayen yan takara da INEC ta fitar babu sunana, kuma babu wani cikin shugabannin jam’iyyar ko jagororin ta da ya yi min gamshen bayani game da halin da ake ciki da Kuma matsayin takarar, an ajiye ne kamar allo, hakan tasa na yanke shawarar barin jam’iyyar”. Inji Alan waka
Ya kara da cewa ya fahimci idan ya cigaba da zama a jam’iyyar a matsayin dan takarar zasu iya karewa a kotu da wanda hukumar zabe ta sanya sunansa a matsayin wanda ta Sani yana takarar dan majalisar tarayya a jam’iyyar a karamar hukumar Nasarawa.
Game da batun ganin da aka yi musu da mataimakin gwamnan kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ala yace dama Gawuna yayansa ne duk da yake basu taba irin Zaman da sukai jiya ba.
” Bayan ficewata daga ADP yan siyasa daga sassa daban-daban sun neme ni, mataimakin gwamnan shi ma ya gayyace ni kuma na je kamar yadda kowa ya gani, amma dai idan lokacin yayi kowa zai ji yadda ake ciki, kuma dama hausawa suna cewa idan kaga kare yana shinshina takalmi to dauke zai yi”. Inji Alan waka
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Aminu Ala yana daga cikin yan Kannywood da suka shi ga jam’iyyar ADP bisa jagorancin Dauda Kahutu Rarara Kuma har aka baiwa wasu daga cikin su takara, amma dai a sunayen da hukumar zabe ta fitar na yan takara babu sunan kowanne daga cikin