Shugabar makarantar ma,ahad Shariff Abdulmajid alhashim tayi kira ga yan’uwa musulmi su dage da nuna kauna ga ma,aiki s a w.
Sidiya fadima Sharif Abdul maid ce ta bayyana hakan a yayin mauludin data shirya na kwanaki hudu domin karanta,Al, qur’ani da ,diwanil da sauran littattafan da suke nuna girma da darajar manzon Allah
Malama Sidiya Fadima ta bayyana cewa nunawa yara darajar manzon Allah shall a w zai taimakawa yaran sanin martaba da girman darajar da yake da ita a wajen Allah subhanahu wa tala
Sidiya Fadima Sharif Abdulmajid alhashim ta kuma mika rokonta ga mata dasu kasance masu hakuri a gidajen mazajensu domin falalar da hakurin yake dashi inda ta bayyana cewa dukkan macen da tayi hakuri a rayuwar aurenta tana samun nasarorin da ba zasu misaltu ba ta yadda zasu zama ababen kwatance.
Sidiyar tace sau tari matan da suka gaza hakurin sune suka fi Shan wahala a rayuwa don haka ya kamata mata su gina ya’yansu akan gwadaben hakuri a gidan aure tun suna yammata.